Fari na kara zama wani abun barazana ga rayuwar mutane, a yanki kasashe masu kusanci da Hamada. A kasar Nijar kuwa, sauki ya fara zuwa. Wajen magance matsalar fari.
Moumouni Abdoulaye, wani makiyayi ne a kasar Nijar, yayi bayanin yadda suke shan wahala wajen ganin sun samar ma dabbobin su ruwa, a irin wannan yanayin.
Su kanyi tafiya mai tsawo cikin hamada, wanda suke saka rayuwar su a cikin mawuyacin hali, domin basu da masaniyar inda suke shiga, ko dai su samu ko kuma su wahala, harma sukan rasa rayuka.
Jama’a a yankin sun fara samun sauki, tun biyo bayan wata gudunmawa, da suka samu daga gwamnatin kasar waje, inda aka basu wayar hannu da radiyo, sukan saurari radiyo, don sanin yadda yanayi yake da irin halin da za’a shiga idan Allah ya kai rai, duk ta hanyar hasashe da ake amfani da na’urori.
Wayar hannu kuwa su kanyi amfani da ita wajen bada rahoton abun dake faruwa a yankin su, hakan kuma yana taimaka musu wajen ganawa da sauran ‘yan uwansu da suke a wani yankin, koda suna da bukatar zuwa wani yanki don shayar da dabbobin su babu wata matsala a yanzu.