Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manhajojin Aika Sakon Gaggawa 2 Na Iya Fuskantar Barazanar Kutse!


Wasu kadan daga cikin manhajojin aika sakon gaggawa, da ke da kwararan matakai, suna iya shiga cikin wasu matsaloli. Wanda hakan zai bama masu kutsen bayanai damar shiga, don dauke bayanan sirrri na mutane.

A cewar wani kamfanin ‘Check Point Software Technologies’ suma manhajojin Telegram da na WhatsApp, dukkan su mallakan kamfanin Facebook suna iya shiga cikin jinsin wadanda masu kutse zasu iya shiga.

A cewar kamfanin sun boye wannan bayanan ne, don jiran sakamakon binciken, sakamakon na nuni da cewar, milliyoyin mutane na iya fuskantar irin wannan kutsen. Hanyoyin da mutane yakamata su bi, don gujema shiga tarkon ‘yan kutse shine.

Duk wani hoto ko bidiyo da aka aiko ma mutun, yayi taka tsan-tsan wajen saukar da shi a wayar shi, domin ana iya amfani da wasu lambobi a yayin saukar da hoton, daga nan sai su sace ma mutun bayanan shi.

Haka wajen aika sakon hoto idan mutun baiyi hankali ba, ‘yan kutsen na iya dauke duk wata dama da mutun yake da akan wayar shi. Hakan zai basu damar juya wayar mutun yadda suke so, da dauke mishi wasu bayanai masu mahimanci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG