Wannan bayanin ya fito ne biyo bayan koken da kungiyar kare rajin dan’adam ta jihar Califonia ta yi.
Kamfanin ya kara da cewa jami’an tsaro na amfani da wata manhajar da ake kira Geofeedia, wajen satar bayanan mutane a shafin Facebook da Twitter.
A cewar mataimakin shugaban sashen bayanan sirri na facebook, Mr. Rob Sherman, daga yanzu babu wata hukuma da za ta sake amfani da shafinsu wajen daukar bayanan mutane, don wani bincike nasu da bashi da alaka da ayyukan kamfanin.
Domin hakkin su ne su kare bayanan mutane, kuma za su yi iya bakin kokarinsu don ganin mutane sun saki jiki da basu amanar bayanansu.
Wannan wani aiki ne da ya rataya akan su, don haka kada mutane su sake samun fargabar daukar bayanansu daga kowace irin hukuma.
Yanzu haka suna kokari wajen samar da tsare-tsare masu ma’ana da karfafa wajen kare bayanan mutane a kowane mataki a shafin Facebook.