Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abubuwan Rayuwar Yau Da Kullun, Da Akafi Siya A Shekarar 2016!


Coca-Cola
Coca-Cola

Kamfanin “Kantar Worldpanel” kamfanin ne da kan bibiyi rayuwar yau da kullun na dan’adam. Kamfanin kanyi amfani da wasu abubuwa na amfanin yau da kullun, wajen gane abubuwa da mutane su kafi siya a tsawon shekarar 2016.

A shekarar da ta gabata, kamfanin sun tabbatar da wasu abubuwan amfani na yau da kullun, a tsakanin mutane a matsayin abubuwan, da akafi siya a fadin duniya. A jerin abubuwan na daya shine, lemun sha na Coka Cola, shine abu da akafi siya, a iya tsawon shekarar da ta gabata.

Abu na biyu kuwa shine, man wankin baki na Colgate, wanda miliyoyin mutane, a duniya su kafi siye. Nagaba kuwa shine maganin kwari na Lifebuoy, wanda kamfanin Unilever kan samar. Abu na gaba kuwa shine Maggi, wanda ake amfani da shi wajen abinci.

A gaba kuwa sai bushashen dankalin turawa, mai suna “Pepsico” haka lemun Pepsi, yabi sahu wajen abubuwa da su kafi kasuwa a shekarar da ta gabata. Nescafe, ya zama abu na bakwai da akafi siye a duniya, nagaba kuwa sai taliyar Indomie itama tasamu kasuwa.

Lemun sha na kamfanin Unilever, kana sai man shafawa na Dove, duk wadannan sune abubuwa, da mutane sukafi amfani da su a rayuwar yau da kullun.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG