Babban kalubalen da na fuskanta a lokacin da na fara waka bai wuce yadda al’umma da iyaye suke kashe mana kwarin gwiwa ba a lokutan da muka shiga harkar waka in ji Bello Vocal.
Matashin mawakin wanda ke rere wakokin Naija hip-hop da ragge hip hop tare da amfani da kade-kaden Afrika wajen rera wakokinsa, ya bayyana cewa daga bisani an fara basu kwarin gwiwa da aka ga sun fara tara kudade , ya kara da cewa da farko wadanda ke cikin masana’antar na basu tsoro baya ga babban kalubalen da suka fuskanta daga wajen 'yan uwa.
Bello Vocal, ya kara da cewa, bayan da ya fara sai ya ga ai ya dace ya fitar da nasa yanayi ko samfurin da zai fita daban da ragowar mawaka, domin ya bada tasa lambar.
Daga karshe babban fatansa dai shine ya tallafa wa matasa mawaka da suka shiga harkar wajen daukaka su tare da muradin ganin ofishinsa ya zama gidan rediyo da zai yayata mawaka.