Facebook ya fitar da rahotansa na karshen shekara wanda ke nuna labaran da suka dauke hankulan mutane a fadin duniya cikin shekara ta 2016.
Hotan bidiyon wata uwa mai suna Candace Payne, shine bidiyon da aka fi kalla kuma yafi daukar hankalin mutane cikin wannan shekara ta 2016 a dandalin Facebook, bidiyon mai taken ‘Chewbecca mom’ ya nuna Candace sanye da fuska kamar ta gwaggon Biri tana ta sheka dariya a motarta.
Sauran batutuwan da suka fi daukar hankalin da kuma wandanda mutane suka fi magana akai sun hada da zaben shugaban kasar Amurka da akayi, wanda Donald Trump ya doke abokiyar karawarsa Hillary Clinton.
Sai kuma danbarwar siyasar kasar Brazil, inda har ta kai ga ‘yan Majalisar kasar suka tsige shugabar kasar Dilma Rousseff a watan Mayu. Daga siyasa kuma sai batun sabuwar manhajar wasan bidiyo wato video game da aka fitar kan wayoyin hannu ta Pokemon Go.
Kungiyar rajin kare ‘yancin bakar fatar Amurka, Black Lives Matter, ta dauki hankulan jama’a wanda aka kafa kungiyar ne biyo bayan yawaita kashe bakaken fata da ‘yan sandan Amurka ke yi. Sai kuma batun kamfen din kashe duk wasu masu mu’amula da miyagun kwayoyi da shugaban kasar Philippines, Rodrigo Duterte, yayi.
Batun wasannin Olympic da kasar Brazil ta fuskanci kaluble wajen shiryawa da gudanarwa kasancewar rikicin siyasar da kasar ta yi fama da shi, shima ya dauki hankulan mutane sosai. Zaben raba gardama kan ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai shima ya zama babban batu da mutane ke magana akai.
Babban wasan kwallon kafar Amurka ta zari ruga, Super Bowl, inda kungiyar kwallon da ake kira Broncos ta bada mamaki wajen doke kungiyar Panthers.
Daga karshe sai mutuwar shahararren mawakin nan da ake kira David Bowie da kuma mutuwar ‘dan wasan damben nan wanda ba a taba kamarsa ba Muhammad Ali, Allah ya gafarta masa. Karshen jerin manyan labaran da suka fi daukar hankli kenan a shekara ta 2016.