Kusan ana iya cewa kowace kasa a fadin duniya, suna da tsare-tsare da dokoki da a wasu kasashe, ba abun damuwa bane. Kamar yadda masu iya Magana kance “Abincin wani gubar wani” A kasar Birtaniya, a shekarar 1986, an gabatar da wata doka, da ta hana kamun kifi mai suna “Salmon” wanda idan aka samu mutun da laifin kama irin wannan kifin, za’a yanka mishi tarar da zata kai $6,500 dai-dai da naira milliyan biyu da dubu dari biyar, ko zuwa gidan kasu.
A kasar China, cikin shekarar 2013, an saka dokar duk wani yaro balagagge da bai ziyarci iyayen shi ba, akai-akai, shima za’a hukun tashi. Kowane d’a dole ya ziyar ci iyayen shi duk bayan kwana biyu, da kuma kokarin taimaka musu, rashin yin hakan zai sa a yanka ma mutun tara ko gidan kasu.
A kasar Ingila kuma idan hukumomin gwamnati suka aika ma mutun da wasika, bayan wasu kwanaki idan mutun bai rubuta amsa ba, shima za’a iya yanka mishi tara da takai $1,300, idan kuma mutun ya karyata amsar wasikar, kudin zasu iya komawa $6,500 dai dai naira milliyan biyu da da dubu dari biyar, ko gidan kasu na wasu shekaru.