Hukumar kwastam ta Najeria karkashin runduna mai kula da iyakar Najeriya dake jihar Legas, ta yi nasarar cafke buhunan ganyen taba wiwi da kudinsa yakai kwatankwacin Naira Miliyan 250, wanda aka yi yunkurin shigo da shi Najeriya daga kasar Ghana.
Da yake jawabi a yayinda ya kai ziyara filin jirgin kasa da kasa na Murtala Muhammed dake Legas, babban kwanturolan hukumar ya bayyana farin cikinsa na wannan gagarumar nasara, da kuma danganta ta da abinda ya kira da kwarewa da gudanar da aiki cikin kyakyawan shugabanci.
Ya kuma kara da cewa, shugaban kwastam na jihar Legas ya jajirce wajan mayar da hankali musamman wajan sa yaran nasa yin aiki tukuru domin tabbatar da dakile fatauci da fasa kwaurin kayayyakin da basu dace ba a daukacin kasar.
Ya bayyana cewa jami’an dake karkashin rundanar Marine command sun kama kayanne a yankin Agbara/Badagry dake kusa da iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, kawo yanzu rundunar ta kama kayayyakin da kudinsu ya kai kwatankwacin kudi Naira Biliyan 3.35 a cikin wannan shekarar.