WASHINGTON D.C —
Fim din ‘There Is A Way’ wani fim ne da aka so a fadada sakonnin da ake son aikawa masu kallo domin kuwa fim ne, da ya nuna muhimmancin ilimin boko.
Wanda ya dauki nauyin fim din Kabiru Jammaje, ya ce an tsara fim din ne domin a nunawa al’umma muhimmancin neman ilimin zamani duk kuwa da dimbin kalubalen da nemansa yake da shi.
Jammaje, ya kara da cewa an tsara fim dinne a harshen Turanci domin canza salon yadda ake shirya fina finai, bayan da ya lura da cewa a Kannywood ba’a taba yin tsintsar fim da ya mayar da hanakali a kan harkar ilimi ba.
Daga karshe ya bayyana cewa ilimi wani muhimmin abu ne da kowacce alumma ko jinsi ke bukata, kuma mafi akasari kasashen da ke Afrika ta yamma ne ke amfani da harshen Hausa.
Ga cikakken rahoton.