Kamfanin jiragen sama na “Air New Zealand” ya sake zamowa kamfanin da yafi kowane, kamfanin jiragen sama zama a kololuwa a fadin duniya. Kimanin shekaru hudu ke nan da kamfanin yake samun wannan nasarar. A shekarar 2017 anyi ittifakin ciwar shine kamfani na daya a duniya.
Kamfanin dai ya samu yabon ne biyo bayan, tsari da suke da shi, wajen shugaban ci da mutunta kwastomomin su, haka da samar da yanayi mai inganci ga duk wanda yake hurda da su. Kamfanin shine kamfani da yake da wasu tsare-tsare da suke kayatar da abokan hurda, wanda mutun zai iya amfani da kyautar makin da suke badawa wajen yin siyayya a ko ina.
Shi kuwa kamfanin “Qatar” shine na ya samu lambar yabo, a kamfanin da yafi tsawon tafiya, da mutunta mutane a ko ina, kuma kamfanin shi yazo na biyu, jerin kamfanoni uku kuwa da suka haye mataki na uku sune “Virgin airlines, Virgin Australia, Virgin Atlantic, Virgin America”
Kamfanin “Emirates” kuwa an zabe shi a matsayin kamfanin da yafi kula da kwastomomi, a lokacin tafiya da da duk wata hurda. Su kuwa sauran kamfannonin da suka shiga sahu, sun hada da Sinagpore Airlines, Cathay Pacific, British Airways, Etihad Airways, All Nippon Airways, Eva Air, a karshe sai Lufthansa.