Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alamar Matattu Ta Bayyana A Shafin Zumuntar Facebook!


Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
Kimanin dubun-dubatan mutane ma’abuta amfani da shafin facebook a fadin duniya, suka fuskanci wani sabon kalubale a shafufukan su. Inda suka fuskanci wata sabuwar alama, dake nuna cewar mutun ya mutu. Dama dai tun a ‘yan kwanakin baya ne, kamfanin suka fitar da wata sabuwar hanya da mutane zasu iya rufe shafin zumuntar face, na ‘yan uwan su idan sun mutu.

Tsarin dai yana bama mutane damar gujema masu kutse a yanar gizo, a duk lokacin da mutun ya mutu, dangin shi zasu iya amfani da shafin nashi da canza tsarin, wanda wata alama take fitowa a shafin da idan mutun ya gani, zai bayyanar da cewar mai wannan shafin bashi a raye.

Abun ban mamaki, sai ga wannan alamar ta fito a shafin shugaban kamfanin na facebook Mark Zuckerberg, wanda ya ga sako da ke cewar “Muna fatar mutane da suke kaunar wannan mamacin, zasu kalli wannan shafin da kokarin tuna mamacin, tare da fatar yi musu addu’a.” Wani mai magana da yawun kamfanin, ya bayyanar da cewar wannan wata matsalace, data faru a sanadiyar wani gyara, da suke kokarin aiwatarwa, amma zuwa yanzu sun magance matsalar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG