Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bada Dadewa Ba Kamfanoni Za Su Fara Kafe Tallar Neman Ma'aikata A Shafin Facebook


Kamfanin Facebook ya fara gwajin wata hanya da zata baiwa kamfanoni damar tallata guraben aiyuka a kan shafin Facebook.

Hakan zai baiwa mutane damar neman aiki kai tsaye a shafin Facebook, ta yadda manhajar zata kwaso bayanai domin saukakawa mutane cike takardun neman aiki ba tare da sun yi kuskure ba.

Kamfanoni zasu iya kafe tallar neman ma’aikata kan shafin Facebook, za kuma su kafe wasu bayanai dangane da aikin, wanda suka hada da yadda aikin yake da albashin da zasu biya.

Wannan yunkuri na nuna yadda Facebook ke kokarin zama wata cibiya ta neman aiki a duniya. Kamfanoni da yawa a baya sun nemi ma’aikata ta kan shafukan sadarwa da suka hada da Facebook, amma wannan yunkuri zai taimaka wajen samar da dangantaka tsakanin kamfanin Facebook da hanyoyin daukar mutane aiki, haka kuma zai zamanto kalubale ga dandalin tallar ma’aikata na LinkedIn, wanda ke samun kudun shigarsa ta hanyar samarwa mutane aiki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG