Shugaban kamfanin Facebook Mark Zackeberg, ya bayyanar da gaggarumar asara da kamfanin yayi cikin awowi biyu 2, biyo bayan kulle kasuwar hannun jari da akayi, bayan faduwar hannun jarin kamfanin. Hakan yasa yawan dukiyar da matashin ya mallaka ta ragu zuwa dallar Amurka billiyan hamsin $50.6B.
A cewar jaridar “Forbes” duk da wannan asarar da matashin yayi, har yanzu yana cikin jerin masu kudi a fadin duniya, inda yake rike da mataki na biyar 5. kuma yana biye da hamshakin tsohon mai kudin kasar Amurkan nan Warren Buffett, da yake mataki na hudu 4.
Kana hamshakin biloniya Carlos Slim Helu, wanda yake mataki na shida 6, yanzu haka dukiyar matashin ta dawo kimanin dallar Amurka, billiyan hamsin da hudu $54.4B. A dai tsakiyar wannan shekarar ne, kamfanin ya samu ribar da ta kai kimanin dallar Amurka billiyan uku da dauri $3.4B.
Zuwa yanzu dai kamfanin ya samu hasarar kusan kashi bakwai 7% na hannun jarin kamfanin. Hakan yasa masu hannun jari a kamfanin cikin damuwa, domin kuwa a shekara mai zuwa ake sa ran, kudaden da ake kashewa a kamfanin wajen hidindimu zasu karu.