Yayin da ake ci gaba da tofa albarkacin baki akan zaben Amurka musamman ganin yadda dan takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Republican Mr Donald Trump ya yiwa jama’ar kasar bazata wajan lashe zaben kasar, jama’a a na cigaba da tofa albarkacin bakinsu.
Ta dalilin haka ne wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Abdulwahab Muhammad ya sami zantawa ta musamman da kungiyar masu sauraron kafofin yada labarai daga jihar Bauchi.
Jama’a da dama sun yi tsammanin ‘yar takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar Democrat Hillary Clinton, ce zata lashe zaben kasar duk da cewa an yi ta kai ruwa rana tsakaninta da takwaranta yayin da suke gudanar da yakin neman zabe.
Mudassiri Tafawa Balewa, sakatare na kungiyar masu sauraren kafafen yada labarai na jihar Bauchi, ya bayyana cewa
“duk da cewa shugaba Obama baki ne, in bayaga shirin koyawa matasa shugabanci bai yiwa Afirka komai ba, dan haka wanene zai taimaki Afirka?”
Saurari cikkakiyar hirar a nan.