Kamfanin Samsung na sanar duk kamfanonin dake sayar da wayoyinsa da su dakatar sayarwa ko musayar sabuwar wayar Galaxy Note 7, har sai ya binciki rahotannin dake nuna cewa itama wayar na kamawa da wuta.
Ranar Litinin kamfanin Samsung ya dakatar da yin wayar bayan fitowar rahotannin dake cewa wayar da kamfanin yake musanyawa wadanda suka sayi wayar farko wadda itama ke kamawa da wuta.
Manyan kamfanonin dake sayar da wayar a Amurka da Australia sun riga sun dakatar da sayarwa ko musayar da wayar, yayin da wasu kamfanonin jiragen sama suka haramtawa mutane shiga jirgi da wayar, bayan da hayakin wata Galaxy Note 7 da aka musanya ta tilasta kwashe daukacin mutane daga cikin jirgi makon da ya kamata a Amurka.
Wayar da aka kera domin ta maye gurbin wadda ke kamawa da wuta ta farko, aka kuma samu ita ma na kamawa da wuta, wannan wani tashin hankali ne ga babban kamfanin da yayi fice a duniya wajen kera wayoyin zamani, kuma ake ganin ya gaza yin maganin halin da kamfanin ya fada wanda zai yi masa wahala kafin ya fito.
Wani jami’in kamfanin Samsung, ya fadawa kamfanin dillancin rabarai na Reuters a safiyar Litinin cewa, kamfanin na yin bincike kan rahotannin da suka fito na cewa wayar na ‘daukar zafi, kuma kamfanin zai ‘dauki mataki cikin gaggawa don ganin ya magance matsalar, ta bin dokar hukumar tabbatar da ingancin kayayyaki.
Ranar 2 ga watan Satumba ne Samsung ya fitar da sanarwar kiranyen wayoyi Miliyan 2.5 na Galaxy Note 7, a dalilin matsalar batiri da aka samu wanda ke yin sanadiyar wayar ta kama da wuta.