Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Ya Tabbatar Da Dumaman Yanayi Ke Haddasa Gobara A Dazuzuka!


Gobara a Dokar Daji
Gobara a Dokar Daji

Bincike da aka zurfafa, ya bayyanar da yadda dumaman yanayi ke harzuka karfin wuta a cikin dokar daji. Tsangayar bincike a harkar kimiyya, sun bayyanar da cewar, kimanin karni uku da suka gabata an kara samun hauhawar karin gobara a cikin dazuzuka, wanda hakan yake da alaka da zafin yanayi tun daga shekarar 1984 zuwa yau.

Binciken ya maida hankali ne wajen yadda kasa ke bushewa, musamman a cikin dokar daji. Wanda suke hasashen hakan a sanadiyar karuwar gobara, a kowane lokaci ta taso a daji. Kimanin kashi hamsin da biyar, na ruruwar gobara a daji na haddasuwa ne akan yadda itatuwa ke bushewa saboda zafi, a sanadiyar rashin ruwa akai-akai.

Tsangayar binciken yanayi a jami’ar Idaho, da jami’ar Gundumar Kwalambiya, duk a nan kasar Amurka, sun tabbatar da cewar mutane suke haddasa bushewar dazuzuka, wajen amfani da kayan zamanin da suke haifar da guba ga tsirrai.

A karshe sun hasashi cewar idan ba’a dauki matakai da suka dace ba cikin gaggawa, wannan annobar ta konewar gandun daji zata cigaba, kuma zata iya zama musiba, ga jama’a a nan gaba kadan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG