Sauyin yanayi yana cutar da masu fama da ciwon Amosanin jini watau “sickle cell” akan haka ne muka sami zantawa da wata matashiya Zahra’u Sani wacce ta ce a wannan lokaci masu fama da irin wannan ciwon da itama ta ke fama dashi na shiga cikin mawuyacin halin.
Ta ce akasarin mafi yawan asibitoci a yanzu idan aka je masu ciwon Amosanin jini ke cika asibtocin, ta ce basa son tsananin zafi, haka ma na sanyi ko sauyin yanayi na zafi-zafin da sanyin-sanyi wani lokacin ma a wannan lokaci na hazo da zafi ya lkan cutar dasu.
Zahra’u ta ce mafi akasari sun lura da ire-iren abinci, suturunsu da kiyayewa da shan magani akan lokaci domin kokarin gujewa safin ciwon cutar da suke fama da ita.
Ta kara da cewa, wani lokacin sai jikinsu ya dinga zafi a wannan lokaci har sai ta kai da an kara musu ruwa ko jini, kafin lafiya ta samu, ta kuma shawarci masu fama da cutar dasu kula da lafiyar su kamar yadda likitoci suka umarta.