Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakin Karatu "Library" Na Zamani Na Taimakama Dalibai Fahimtar Karatu!


Dakin karatun dalibai Library
Dakin karatun dalibai Library

Mafi akasarin jami’o’I da kwalejojin kimmiya da fasaha a nan kasar Amurka, sun dauki wata sabuwar azama wajen ingantawa da kayatar da dakunan karatu na “Library” a turance.

Yawancin laburari a makarantu na wannan zamanin, karni na ashirin da daya 21, suna dauke da wasu abubuwa da suke taimakama dalibai wajen fahimtar karatu, da rayuwa baki dayan ta.

A cikin dakunan karatu na wannan karnin, za’a samu wajen hutawa da shakatawar dalibai, wanda dalibai zasu zauna don tattauna wasu abubuwa, da suka shafi karatu da ma rayuwar yau da kullun.

Haka an kayatar dasu da kujerun alfarma, wajajen laka kwanfutocin zamani da wayoyi, haka akan ware wasu gurare da ba’a son yin magana, waje ne kawai masu bukatar karatu batare da hayaniya kan zauna a wajen. Akwai duk wasu na’urori da zasu taimakama dalibai wajen nasara a karatun su. Akan samar da kafar yanar gizo na tsawon awowi ashirin da hudu.

Yawancin littatafai akan same su a yanar gizo, babu dalili da sai dalibi yaje dakin karatu kamun ya samu damar karanta littafi, dalibai dubbai kan iya karanta littafi daya a lokaci daya. A wannan zamanin laburari basa cika da yawan takardu saboda cigaban yanar gizo.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG