Kwamitin da gwamnatin jihar Adamawa ta kafa domin ya binciki zargin da aka yi na wani likita da ya cirewa wani matashi koda guda ba tare da izini ba ya mika sakamakon binciken.
Shugaban kwamitin Dr Pius Tizhe, a yayin da yake mikawa kwamishiniyar lafiyar jihar Dr Fatima Atiku sakamakon binciken a Yola, ta ce kwamitin yayi aiki mai nigari.
An gudanar da bincikenne akan wani likita wanda aka sakaya sunansa dake wani asibiti mai zaman kansa a Jimeta, da cirewa wani matasahi mai shekaru 23, da haihuwa mai suna Isa Hamman daga karamar hukumar Fufore koda ba tare izini ba.
An zargi likitan da cirewa matasahin koda wanda daga baya ya sake tura mara lafiyar babban asibitin gwamnatin tarayya dake Gombe domin ci gaba da jiyya.
Mujallar Daily post ta wallafa cewa kwamishiniyar ta yabawa kwamitin akan kokarin da suka yi, ta kuja kara da cewa mikawa gwamnan jihar Muhammad Bindow sakamakon binciken domin daukar dukkan matakan da suka dace