Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Masu Neman Aikin Immigration Sun Yi Zanga Zangar Lumana A Fadar Shugaban Kasa


A fadar gwamnati dake babban birnin tarayya Abuja, wasu gun gun matasa wadanda aka dauka aikin shigi da fice na kasa wato immigration da aka dauka aiki a shekarar data gabata sun gudanar da zanga zanagar lumana domin matsawa shugaba Muhammadu Buhari ya tilastawa ma’aikatar su ta basu guraben da zasu fara aiki, ganin cewa sun yi horon da ya kamata su yi tun bara amma ba a basu guraben ayyuka ba.

Wakilin sashen Hausa na muryar Amurka ya yi tattauna da wasu daga cikin matasan a yayin da suke gudanar da zanga zangar wadda suka tare wani bangare na shiga fadar gwamnati inda suka bayyana dalilansu na yin wannan zanga zanga.

Daya daga cikin matasan ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin cewa a mayar da matasan domin su cigaba da aiki amma ministry of interior da hukumar daukan ma’aikatan suka bada sanarwar sake tantance matasan a wata ganawa da suka yi da manema labarai, kuma a halin yanzu a cewar matasan, hukumar na kiransu da suna masu neman aiki a maimakon wadanda aka dauka aiki duk da cewa sun kammala dukkan horon da yakamata su yi.

Matasan sun kara da cewa suna kyautata zaton zanga zanagar zata sa shugaba Muhammadu ya saurare su domin share masu hawaye.

Domin Karin bayani saurari rahoton Umar Faruk Musa daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG