WASHINGTON, DC —
A shirinmu na mata da suke taka rawa a cikin al'ummarsu a yau mun sami zantawa da malama Bilkisu Adamu ma'aikaciyar a ma'aikatar ayyuka da gidaje, ta ummarci mata dasu tashi tsaye domin neman ilimi.
Malam Bilkisu, tace ya zama wajibi ga mata a wannan zamani da muke ciki su tashi su dukufa neman ilimi koda kuwa baza suyi aikin gwamnati ba .
Tana mai cewa ilimi na taimakawa gaya wajan tarbiyar yara dama tafiyar da harkokin gida da zamatakewa tsakanin iyalai da makwabta.
Ta ce a tasowarta ta so ta zama ma'aikaciyar lafiya amma hakan bai samu ba, amma saboda mahimmancin ilimi sai ta ci gaba da abinda aka dorata akai wanda ya kasance ilimin lissafi.