Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salisu Abdullahi: Rayuwa Da Karatu A Amurka Sunfi Na Koina!


Salisu Abdullahi
Salisu Abdullahi

Salisu matashi dan Najeriya, dake karbar horaswa a nan kasar Amurka, yana cigaba da bayyana alfanun dake tattare da wannan zuwan nasu kasar Amurka. Akwai matasa da suke gudanar da ayyuka da kasuwanci kala-kala, gwanin sha`awa wanda muka hadu a nan Amurka, da ma yan uwana yan Nijeriya, wanda muka tattauna kafin mu tafo nan Amurka. Hakika, zabin da akayi yana nuni da cewa wannan zangon matasa zasu iya kawo canjin da ake bukata a shekaru masu zuwa a gida Nijeriya da ma Afrika baki daya.

Akwai banbanci mai yawa tsakanin karatun Nigeriya, da kuma na nan Amurka, wadanda suka hada da. Abinda karatun ya kunsa kayan karatu, dukkan abinda karatun ya kunsa a nan kamar yanda na lura dai abu ne wanda yake da alaka da abinda yake faruwa kai tsaye a zamanance a duniya, ba wai abunda ya jima da shudewa bah, ko an ma daina amfani da shi a zamanance. Karatu a Nijeriya, mafi yawa wani lokacin yana kunsan abinda bashi da alaka ko amfani da abinda ke faruwa a duniya a zamanance.

Alaka mai kyau da gabatar da karatu mai gamsarwa tsakanin malamai, farfesoshi da kuma daliban su. Na gamsu sosai da yanda manya manyan farfesoshi ke bada kulawa da kuma son taimakawa mutum akan abinda yake nema, yake so ya sani, ko ya kawo shi. Suna da kirki sosai da sosai, da son bada gudunmawar su, iya wajen da karfin su ya kare. Har sai mutum ya gamsu kuma ya gane abinda suke koyarwa, wannan sabanin abinda yake faruwa a kasarmu Nijeriya ne, da yawa wasu zasu ce maka basu da lokacinka, wasu ba zama su saurareka bah, wai don su farfesoshi ne.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG