Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasan Game Na Wayar Hannu “PokemonGo” Ya Shahara A 2016!


Wasan Kwamfuta Mai Kwakwalwa!
Wasan Kwamfuta Mai Kwakwalwa!

Nishadi ko kuwa tabuwa? Tun a farkon wannan watan da aka kaddamar da wani sabon game, da mutane kan buga a wayoyin su na hannu, milliyoyin mutane sun shiga wani sabon hali, na rashin natsuwa. Shidai wannan game din mai suna “Pokemon Go” yana tattare da wasu aljanu da sukan daukema mutun hankali a yayin buga wasan.

Wasan kan ba mutun damar fahimtar wasu garuruwa ko kasa da mutun bai taba ziyarta ba, a duk lokacin da mutun yake buga wasan, zai dinga tafiya daga wani birni zuwa wani, kuma yana dauke da wasu manhajoji da ke daukar hankalin mutun a duk lokacin da yake buga wasan.

Shine game na farko da ke dauke da taswirar duniya na gaske “World Map” a turance, haka ana iya amfani da wannan game din wajen daukar hoton mutun tare da na aljanun wasan game din. Yana dauke da wasu aljanu da sukan taimaka ma mutun wajen kama wasu aljanun don horar da su ta yadda mutun yake bukatar suyi wasa. Yanzu haka dai mutane da dama a fadin duniya na buga wannan wasan a kowane lokaci.

Mutun zai iya kama wasu aljanun don horar da su yadda yake so, haka mutun zai iya zabar aljani daya ya zama kamar shine shugaba da bada umurni ga sauran ‘yan wasa. Akan samu mutane da dama suna buga wannan wasan a yayin da suke tafiya kodai a kan titi, har wasu kan buga wasan suna cikin mota, wanda hakan ya haddasa haddura da dama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG