WASHINGTON DC, —
Jim kadan bayan samun rahoton wasu masana da suka tashi daga
wannan duniyar, zuwa duniyar watan Jupiter, sai ma’aikatan
hukumar NASA, suka fara rungumar juna da murna. Wannan yana nuna
irin nasarar da suka samu, wanda a tarihin duniya babu wani
mahaluki da ya taba kusantar wannan duniyar.
Ita dai duniyar Jupiter, itace duniya da tafi kowace duniya hadari wajen kusantan, don tana kusa da Rana, tana zagaye da wata irin karsashin wuta, da wata irin iska mai gurnani da duk wasu irin abubuwa da zaisa babu abun da zai iya kusantar ta. Amma a wannan karon, masana sun kwashe shekara da shekaru don bincike akan ya wannan duniyar take, da kuma taya za suyi don kaiwa gareta.
Bayan kwashe watanni ashirin 20, ana shirye-shiryen zuwa duniya, sai gashi haka ta cinma ruwa. Acewar shugaban binciken Mr. Scott Bolton, yanzu haka dai masanan suna cikin duniyar, inda za suyi amfani da wadansu ma’aunai don kiyasta yanayin duniyar, domin duniyar tafi duniyar nan tamu ta mutane da kimanin kashi sama da dubu ashirin karfi.