Bayan wani zaman tattaunawa har na tsawon mako guda da hukumar jarabawa ta JAMB tayi da manyan ma’aikatan jami’oi dana sauran manyan makarantun gaba da sakandire na Najeriya, hukumar ta bayyana fito da sabon tsarin dabarun daukar sababbin dalibai masu shiga jami’a kai tsaye daga.
A cewar bayanan da ta wallafa a shafinta na yanar gizo jiya a daren litini, hukumar jarabawar ta bayyana cewa sabuwar dabarar ne bisa abinda ta kira (Pint System).
A yayin da ta bayyana yadda dalibai zasu sami shiga jami’a bayan daukar jarabawar da kuma wadanda za’a dauka kai tsaye wato direct entry, hukumar ta bayyana cewa jami’oi zasu caji dalibai kudaden tanttancewa bayan hukumar JAMB din ta basu kafar fara karatu a jami'ar.
Kafin jami’a ta dauki kowane dalibi, wajibi ne dalibi ko daliba su kasance sana da takardar shiga jami’ar wadda hukumar jarabawar ta JAMB zata fara badawa.
Dan haka kwanan nan hukumar zata fitar da hanyoyin da dalibai zasu bi domin duba sunayensu ta yadda zasu iya ganin ko sun sami shiga jami’ar da suka zaba a yayin da suka rubuta jarabawar ko a’a maimakon zuwa ko dogaro akan jami’ar. Dan haka dalibai sai kuyi ta du’a’i a cewar hukumar ta JAMB.
Daya daga cikin abinda zai karawa dalibi kwarjini ga jami'ar da yake neman shiga shine yanayin sakamakon jarabawar kammala sakandire, wato daliban da suka bada sakamakon jarabawa guda a maimakon biyu zasu sami maki goma daga cikin adadin yawan makin da ake bukata kai tasye.