Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Wayoyin “Apple” Zai Fuskanci Sabuwar Turjiya!


Kamfanin Wayoyin Apple.
Kamfanin Wayoyin Apple.

Kamfanin wayoyi na “Apple” zai shiga cikin tsaka mai wuya. Kamfanin dai yana kokarin saka wata katanga ga masu daukan hoto ko bidiyo a lokacin da suka shiga cikin jama’a. Yunkurin su shine a duk lokacin da mutune suka shiga jama’a kada suyi amfani da wayar su don daukan abun da akeyi. Zasu sakama wayar su wata manhaja wadda idan mutun yana cikin taro kyamarar daukan hoton wayar shi bazata yi aiki ba.

Mutane da dama nata korafi dangane da wannan matakin na kamfanin, domin kuwa suna ganin kamar an shiga cikin hakkin su na bama kowa damar yin abun da yake so. Da dama naganin cewar hakan zai sa kamfanin rasa kwastomomi, domin babu wanda zai yadda a dinga tsara mishi yadda zaiyi da rayuwar shi.

Dalilin da yasa suke wannan kokarin shine, kamfanoni da dama na kuka da yadda mutane kanje wajen taro wanda suka biya kudi suka shiga kamar filin kwallo, ko gidan kallon fitattun mawaka, sai mutane su dinga amfani da wayar su, suna daukan bidiyon yadda ake gudanar da shagalin.

Suna sawa a shafufukan su na zumunta facebook, twitter, instagram, da dai makamantan su, wanda hakan zaisa wasu da basu biya kudi sunje wajen ba, suga abun da yake faruwa. Suna ganin hakan shi ke sa wasu mutane rasa kudi akan wasu harkokin kasuwancin su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG