Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ake Gudanar Da Bukukuwa Sallah A Amurka!


Sallah A Kasar Amurka
Sallah A Kasar Amurka

Masu iya magana kance "Sallah bukin rana daya" kimanin milliyoyin mutane suka ziyarci masallatan idi, a baki daya kasar Amurka. Kamar yadda addinin musulunci ya tanada, bayan kammala azumin watan Ramadana, musulmai kanje masallacin idi don gabatar da sallar idi.

A nan kasar Amurka ma, ba'a bar musulmai a baya ba. Wakilin DandalinVOA Yusuf Aliyu Harande, ya ziyarci karamar hukumar Indian a jihar Pennsylvania a kasar Amurka, inda ya samu zantawa da wasu musullmai.

A masallacin akasarin mutanen dake masallacin 'yan kasashen waje ne, sukan gudanar da bukin sallar su dai-dai al'adun su. Abun sha'awa da kauna shine, yadda mutane da su kazo daga wasu kasashe daban-daban a fadin duniya kan hadu da wasu, da kawo abinci iri daban daban don kara dankon zumunta.

Yara kuwa akan sa musu kaya irin na kasar su, da bada goron sallah ga yara wanda suka hada da kayan ciye-ciye da abubuwan wasa. Daga bisani kuma jama'ar karamar hukumar kan hadu da sauran jama'a, na yankin da suka hada da musulmai da ma wadanda ba musulmai ba, don kyautata dangantaka, hakama sukan daho abincin kasashen su don nuna irin nasu al'adun da kaya haka da abinci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG