A gobe ne idan Allah ya kaimu wani kamfanin wayoyi a kasar India zai kaddamar da wata wayar “Smartphone” da suka kirkira da tafi kowace waya arha a fadin duniya. Wannan kamfanin mai suna “Ringing Bells” zasu fitar da wayar tasu a kasuwa mai suna “Freedom 251” Sun bayyanar da wayar na dauke da manhajoji da dama da tsari kamar na wayar IPhone 5.
An kiyasta kudin wayar kasa da dallar Amurka $4 dai-dai da naira dubu daya N1,000 ita dai wayar tana da kyamarar gaba da ta baya, da girman inci 4, kana tana dauke da girman ciki 1GB, da girman kwakwalwa 8GB, haka tana da gurbin aika sakon gaggawa na email, tana dauke da kusan duk wasu abubuwa da manyan wayoyi suke dauke da, har da su jin wakoki.
Kamfanin dai ya bayyanar da cewar wannan wayar itace wayar smartphone da zatafi arha a fadin duniya, suna sa ran kaddamar da wayan a ranar Juma'a 7, ga wannan watan. Kasar india itace kasa ta biyu a duniya da sukafi cinikin wayoyi. Amma abun tambaya a nan shine wai kuwa kamfanin zai iya samar da milliyoyin wayar don isan mutane a fadin duniya?