Ba kamar yadda aka saba a al’adance ba, wato a wannan karon sarkin musulmi bai bayar da sanarwa da kansa ba, illa rubutacciyar sanarwa da aka rarrabawa ‘yan jarida da suka taru a fadar mai alfarma sarkin musulmi.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kwamiti mai ba majalisar sarkin musulmi shawara akan harkokin addinin musulunci farfesa Sambo Wali Junaidu, tace dukkan rahotannin da aka samu daga shugabanni da kungiyoyinh addinin musulunci da kwamitocin duban wata na kasa dana jihohin Najeriya sun nuna cewa babu inda aka sami ganin jinjirin watan shauwal a jiya lahadi, wadda itace ranar 29 ga watan Ramadan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sarkin musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar wanda shine shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya, ya aminta da wannan rahoton domin akan haka yayi matsayar cewa watan Ramadan na wannan shekara yayi farilla, wato ya cike kwanaki talatin Kenan.
Dan haka ranar laraba idan Allah ya kaimu ce zata zama daya ga watan shauwal, kuma ranar ce ‘yan Najeriya zasu gudanar da bukukuwan Eid ul fitr na wannan shekara ta 2016.
Saurari cikakken rahoton.