WASHINGTON D.C —
A bangaren saye da sayarwa da zawarcin zaratan ‘yan wasan kwallon kafa, kungiyar Arsenal ta sayi dan wasan kasar japan mai suna Takuma Asano mai shekaru 21 da haihuwa.
Leicester city kuma ta bayyana ra’ayinta na sayen Nempes Mendez dan shekaru 24 da haihuwa har na tsawon shekaru hudu.
Ita kuma Manchester United tana dab da sayen dan wasan Croatia Herik mai shekaru 25 da haihuwa da kuma bayyana aniyarta ta sayen dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic a matsayin kwantaragi na tsawon shekara guda.
Idan muka koma kungiyar Chelsea kuma, ta kammala sayen dan wasan kasar Belgium Mudingayi dan shekaru 22 da haihuwa.