Kasar Faransa da yanzu haka ke karbar bakuncin wasannin kwallon kafa na cin kofin nahiyar Turai ta sami kaiwa wasan kusa dana karshe wato Semi-final na wasan, bayan ta lallasa kasar Iceland da zunzurutun ci 5 - 2 a wasan na kwata final da suka fafata.
Saboda haka idan Allaha ya kaimu ranar alhamis Faransa zata yi karon battar karfe da kasar Jamus a wasan kusa dana karshe, ita dai Jamus ta sami kaiwa wannan matakinne bayan ta doke kasar Italiya da ci 6 - 5 a bugun fenariti bayan da wasansu ya tashi a kunnen doki da ci 1-1.
A bangare daya kuma kasar Portugal zata kara ne da kasar Wells a daya wasan kusa dana karshe, Portugal ta sami kaiwa wasan na kusa dana karshe karo na hudu a wasanni biyar bayan da ta doke Poland da ci 5 - 3, suma a bugun fenariti bayan tashin wasan da ci 1-1.
Wannan ne karo na farko da Wells ke fafatawa a gasar, domin haka tana kokarin kafa sabon tarihi ne akan wasanta daya gabata inda Belgium ta doke ta da ci 3-1 a wasansu na kwata final
A kasar Ingila kuma kungiyar zakarun gasar Premier Leicester city ta cimma matsayar rattaba hannun kwantaragi da dan wasan gaba na Najeriya Ahmed Musa, dan shekaru 23 wanda yake bugawa kungiyar CSK Moscow wasa tun daga shekarar 2012 inda ya zura mata kwallaye 54 a cikin wasanni 168.
Danna nan domin Karin bayani.