A shirin yau da gobe shirin matasa da ya gabata, shirin ya tattauna ne akan dangantaka dake tsakanin yara da iyaye da kuma nuna soyayya fiye da kima da wasu iyaye ke nunawa yara, da kuma yadda hakan ke shafar tarbiyar yara.
Kamar yadda babban bakon shirin ya bayyana, yanzu zamani ya canza da koya tarbiya ya zama abin da yazama, domin kuwa da zarar yaro yayi korafi akan wani abu zaka ga iyaye sun fara tarairayar sa al’hali a lokuta da dama laifin yaronne.
A cewar babban bakon, kamata yayi idan yaro yayi laifi ba lallai sai an doke shi ba, idan aka bishi da lalama aka fahimtar da shi akan cewar abinda ya aikata bai dace ba, sa’an nan kuma idan yayi abu na alkhairi a yaba masa, domin a koda wane lokaci zai so ya maimata abinda yayi ya sami yabo.
Cika nuna wa yara soyayya yakan sangarta yaro, yana sa yara su zama shagwababbu wadanda daga karshe basa iya kullawa kawunansu komi balle su taimakawa na baya dasu wadanda daga karshe idan aka rasa iyayen sai su sami kawunansu cikin halin kaka nikayi.
A kwai tausayawa da ta kamata iyaye su nunawa yara amma kada kauna da soyayyar da iyaye zasu nunwa yaro tasa ya sangarce.
Saurari cikakkiyar hirar anan.