Rundunar ‘yan sandan jihar Niger a tarayyar Najeriya na can na gudanar da bincike akan wata matshiyar matar aure ‘yar shekaru goma sha bakwai da haihuwa mai suna Bara’atu Muhammad da ta sanaya wuka ya yanke mazakutar dandan kishiyarta mai suna Buhari Muhammad wanda aka Haifa kwanaki 23 da suka gabata.
Wannan al’amari da ya faru a karamar hukumar shiroro,a kauyen Dape dake yankin karamar hukumar yayi matukar tayar da hankalin mazauna yankin a lokacin da aka kawo wannan mata Bara’ayu data yi wannan danyen aiki a shalkwatar ‘yan sanadan jihar Niger, a zantawar da wakilin sashwn Hausa na muryar Amurka yayi da matashiyar inda ya tamabaye ta ko tasan abinda ya sa aka kawo ta ofishin ‘yan sanada sai ta bayyana cewa ;
“Na yi laifi shiyasa aka kawo ni nan, domin na yanke wa jariri mazakuta da wukar da na dauko daga daki na, kuma naje bayan gida ne inda na yanke masa mazakutar kuma na barshi can a bayan gidan”.
Matashiyar ta bayyana cewa bata ji dadin abinda ta aikata ba amma ta bukaci ganawa da mijin nata.
A halin yanzu dai yaron na kwance a asibitin kwararru na IBB dake Minna inda Dr Ibrahim Abdullahi likitan dake kula da yaron ya bayyana cewa babban rauni ne kuma a lokacin da aka kawo yaron asibitin, mazakutar ta riga ta mutu domin kuwa ta yi bakikkirin, kuma a cewar sa babu asibitin da za’a iya mayar da ita a fadin kasar.
Mahaifin yaron mai suna Muhammad Dauda ya ce watanni hudu Kenan da ya auri Bara’atu kuma a iya sanin sa bata da wani tabin hankali, sa’annan bait aba samun sabani da it aba.
A yanzu dai ma’aikatar da ke lura da harkokin hakkin yara ta jihar Niger tace ta dauki nauyin bin ba’asin wannan lamari harma da bada gagarumar gudummuwa wajan daukar nauyin magani na wannan yaro.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.