Shugaban Najeriya, ya nada AIG, Ibrahim, K. Idriss, a matsayin sabon Sufeto janar na ‘yan Sandan Najeriya, biyo bayan ritayar Mr. Solomon Arase, daga aiki.
An haifi Ibrahim Idriss, a garin Kutigi, dake karamar hukumar Lavun a jihar Neja, a shekarar 1959, bayan ya kamala digirin san a farko a jami’ar Ahmadu Bello, dake Zaria, yayi dighiri na biyu a bangaren aikin lauya a jami’ar Maiduguri.
Ibrahim Idriss, ya shiga aikin dan Sanda, zamanin mulkin Buhari na mulkin Soja a shekarar 1984, ya shafe shekaru 17, yana bangaren ‘yan Sandan kwantar da tarzoma, ya rike mukaman da dama,
Ya kuma yi kwamishinan ‘yan Sanda a jihohin Nasarawa da Kano, sanan ya reke shugaban ‘yan Sandan kwantar da tarzoma a hedkwatar ‘yan Sandan Najeriya, ya kuma yin aiki a rundunar ‘yan Sandan majalisar dikin duniya dake Liberia da Istimo, inda har shugaban kasar ya bashi lambar yabo.
Sabon sufeton janar na ‘yan Sandan Najeriya, yace zasu yi aiki tukuru domin ci gaba da kare dukiya da rayukan ‘yan Najeriya, Kuma ganin cewa akwai manya manyan jami’ai, dake gaban Ibrahim Idriss, a rundunar ‘yan Sandan Najeriya, da kuma yanzu za suyi ritayar dole abinda tsohon mataimakin sufeton janar na ‘yan Sandan Najeriya Ibrahim Baba Ahmed, wannan bai dace ba.