Taron, na makon mata da jarirai ne, na tsakiyar shekara da hukumar kiwon lafiya matakin farko ta Abuja ta shirya.
Abun da ya fi daukan hankali a taron shi ne alkaluma na mata 576 da kan mutu cikin mata 10,000 yayinda suka zo haihuwa a Najeriya. Haka kuma mata kashi 17 cikin 100 ne kacal ke shayar da 'ya'yansu da nonon uwa a Najeriya sabanin kashi 76 na matan dake shayar da 'ya'yansu da nonon uwa a kasar Ghana.
Dr Rukaya Wamako babbar jami'a a hukumar kiwon lafiyar tace idan mace mai juna biyu tana zuwa awo a asibiti za'a iya gano damuwarta da wuri. Damuwar da za'a iya tsareta domin kada ta yi wani aibu za'a tsareta. Wadda kuma ba'a iya tsareta ana iya yin kariyar da zai hanata zuwa da tsanani. Zuwa asibiti na taimakawa a kare mata daga mutuwa lokacin haihuwa ko raba jariransu da samun wata nakasa.
Babban sakataren hukumar Dr. Rilwanu Muhammad ya yi karin bayani kan sinadarin dake kara karfin gani.Ya bayyana irin magungunan da ake ba yara ya hanasu amai da gudawa da kuma kara masu karfin jiki. Haka kuma yana basu karfin ido da fatar jiki.
Baicin haka, inji Dr Rilwanu, ana nuna wa matan yadda ake kayyade iyali wajen haihuwa. Ana kuma yin binciken cututtuka kamar su sida domin a dauki matakan da suka dace a boye domin bada magani.
Wata budurwa ma da ta kammala karatu mai suna Blessing Zango da ta halarci taron tace ita kam idan ta yi aure zata ba 'ya'yanta nono yadda ya kamata saboda shayar da yara nono na akalla watanni shida, na kawar da cututtuka da dama.
Maza ma sun kasance a taron. Shugaban kungiyar masu lalurar shan inna na Najeriya , Musbahu Lawal, yace ya kasance wurin ne a matsayinsa na magidanci ya koyi wasu abubuwa da zai karawa iyalansu kaimi domin tabbatar da cewa an yiwa 'ya'yansu allurorin rigakafi da suka dace.
Ga karin bayani.