'Yansandan na aikin bayar da kariya ne ga wata motar safa a garin Elwak, daura da kan iyakar Somaliya, yayin da 'yanbindiga suka harbi motarsu da abin da ake ganin gurneti ne da ake harbawa da roka.
"Mu na masu yin tir da harin da al-Shabab ta kai a Dimu da wannan safen, inda jami'an 'yansanda biyar su ka mutu," a cewar gwamnan Karamar yankin Madare a shafin Twitter dinsa.
Al-Shabab, wadda tamkar reshen al-Qaida ce a gabashin Afirka, wadda cibiyarta na Somaliya ne amma takan kai hare-hare cikin Kenya. Kan iyakar Kenya da Somaliya babu ingantaccen tsaro saboda nisarta da kuma rashin hadin kai tsakanin jami'an tsaron kasashen biyu.