To saidai tambaya nan ita ce me ya jawowa bakunan Najeriya hasar ribar da suke samu da can saboda a lokacin Farfasa Soludo an tilasta masu su kara jari lamarin da ya sa wasu bankuna suka hade, suka dunkule, suka zama daya domin samun ingantacen jari wanda aka tsayar kan nera biliyan 25 kowane banki.
Haka ma a lokacin Shugaba Jonathan, babban bankin Najeriya ya samu wasu shugabannin bankuna da laifi har aka gurfanar dasu gaban kotu.
Ra'ayin masana tattalin arzikin Najeriya ya zo daya. Sun nuna cewa dama can bankunan Najeriya na dogaro da kudin gwamnati. Da shugaba Buhari ya kama mulki sai ya janye kudaden gwamnati daga bankunan kasuwa lamarin da ya jefasu cikin wani halin kakanikayi. Kirkiro da asusu daya da gwamnati ta yi wanda ake kira TSA yana cikin dalilin da ya sa suka shiga matsala.
Yushau Aliyu wani masanin tattalin arziki yace bankuna da sun dogara ga ma'aikatun gwamnati su kawo masu kudi kana su, su zubawa gwamnati caji. Shi ma Abubakar Ali yace bankuna sun bar aikin banki sun koma karban kudi a hannun gwamnatocin tarayya da na jihohi da na kananan hukumomi da kuma masana'antun gwamnati.
Aikin banki ne ya rike kudin jama'a, ya karbi kudin jama'a kuma ya sake mayarwa jama'a kudaden ta hanyar basussukan da jama'a ke bukata domin inganta harkokin kasuwancinsu da nufin bunkasa tattalin arziki.
Ga karin bayani.