Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Amurka Ya Bar Dokoki da Suka Haramta Mallakar Wasu Bindigogi


Loretta Lynch, sakatariyar shari'ar Amurka
Loretta Lynch, sakatariyar shari'ar Amurka

Kotun kolin Amurka ta kyale dokoki biyu na haramta wasu daukan muggan bindigogi shigin na yaki da kuma bindigogi masu sarrafa kansu, kamar yadda wasu jahohi biyu su ka bukata.

Masu son a bar 'yancin mallakar bindiga sun kalubalanci dokar haramta bindigogi shigin na yaki a Connecticut da New York, to amma jiya Litini, kotun ta ki sauraren karar.

An kafa dokokin hana nau'in bindigogin ne bayan da wani dan bindiga sabe da bindiga samfurin AR-15 ya kashe wasu yara 20 da malamai 6 a wata makaranta a Newtown, jihar Connecticut a shekarar 2012.

Jahohi 7 da birnin Washington DC, sun kafa dokokin haramta bindigogi shigin na yaki. Tun da ma dokar tarayya ta harmata mallakar bindiga mai sarrafa kanta.

Muhawara kan damar mallakar bindiga ta sake tashi ne bayan wani harin da aka kai a farkon wannan watan a wani wurin shakatawar 'yan luwadi da dare a Orlando, jihar Florida wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 50, ciki har da dan bindigar.

XS
SM
MD
LG