Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar India Ta Musanta Zargin Tabarbarewar Addini A Kasar


Ma’aikatar harkokin wajen India ta ce ba ta yarda da wannan rahoton ba

Kasar India ta musanta zargin da wata hukumar ta Amurka ta yi akan cewa ‘yan cin addini ya tabarbare a kasar.

Hukumar ta Amurka, akan ‘yancin addini ta kasa-da-kasa da ake kira USCIRF a takaice, kwanan nan ta fadi cewa mutunta addinan juna ya tabarbare kuma muzanta ‘yancin addini ya karu a kasar ta India a cikin shekarar da ta gabata.

Ma’aikatar harkokin wajen India ta ce ba ta yarda da wannan rahoton ba, wanda ta ce bai nuna akwai fahimtar kasar ba, da al’ummarta da kuma kundin tsarin mulkinta.

India kasa ce mai jinsina da yawa wadda aka kafa ta akan turbar dimokaradiyya mai karfi. Kundin tsarinmulkin kasar ya yarda da kare ‘yancin bi’adama a kasar, ciki har da ‘yancin addini, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Vikas Swarup.

Rahoton na hukumar USCIRF ya fadi cewa tsirarun al’ummar kasar musamman Kirstoci, da Musulmai, da mabiya addinin Sikh, sun fuskanci cin zarafi, muzanci da tashin hankali lokuta dayawa, yawancin kuma a hannun kungiyoyin mabiya addinin Hindu na kasar.

XS
SM
MD
LG