Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa 'yan koren 'yan siyasa na korafi da rashin samun wurin dafawa bayan zabe


Mata, Maza, Matasa suna murnar nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaben 2015
Mata, Maza, Matasa suna murnar nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaben 2015

Matasan da suka yi fafutikan ganin jam'iyyar APC ta samu nasara a zabukan da aka yi a Najeriya yanzu suna kokawa da yadda aka barsu babu abun yi ,sun zama tamkar maroka a ofisoshin jam'iyya ko kuma gidajen 'yan siayasa da suka ci nasara a aben baya

Yayin da saura ‘yan makonni gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi su cika shekara da karbe madafun mulki, matasa da mata da suka taimaka wajen yakin neman zabe sun ce har yanzu basu gani a kasa ba.

Wakilin Muryar Amurka ya yi nazarin makomar irin wadannan matasa da mata wadanda ke safa-da-marwa sakanin ofisoshin jam’iyun siyasa da gidajen zababbu da masu rike da mukaman siyasa da kokon bara suna maula domin neman abin biyan bukatun rayuwa na yau da kullum.

Shugaban ma’aikata na ofishin gwamnan jihar Adamawa Alh. Abdulraman Abba ya fada a hirar da na yi da shi cewa kawo yanzu akwai matasa da mata dari biyu dake aikin share manyan tituna a Yola fadar jiha a matakin gwaji da niyyar fadada shirin zuwa wasu kananan hukumomi.

Na tambayi mataimakin shugaban jam’iyar APC mai mulki Alhaji Mohammed Abdullahi ko wane tanadi jam’iyar ta yi domin matasa da mata, ya yi alkawarin nan da ‘yan watanni biyu masu zuwa zasu sa’ida.

Duk da abun da ya fada matasa da mata suna korafi, sun cewa an barsu kuma kawo yanzu basu ci ribar yakin da suka yi ba.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG