Jami'an Amurka sun dage cewa,kungiyar taji jiki matuka, kuma babu ma lokaci da ake ganin kasawarta kamar yanzu tun bayan da tayi kutse cikin kasar Iraqi a shekarar 2014. Duk da wannan, jami'an tsaro da bangaren masu aikin leken asiri, suna gargadin cewa a yi hattara kungiyar tana da kwarin guiwa duk da matsaloli da take fuskanta.
Da asubahin jiya ne ISIS ta kaddamar da hare haren, wadanda ta auna kan mayakan kurdawan a arewa da kuma kudancin birnin Mosul, inda tayi amfani da manyan makamai ciki harda da motoci da aka dankarawa nakiyoyi da kuma 'yan kunar bakin wake.
"Gagarumin hari ne, inji janar Hamid Afandi, na dakarun kurdawa, da yake magana kan farmakin da kungiyar ISIS ta kai a wurin da ake kira Telskurf, mai tazarar kilomita 30 daga arewacin birnin Mosul. ISIS ta kama iko a yankin na sa'o'i biyu zuwa uku.
Sai dai jami'an kurdawa sun kira harin da ISIS ta kai har ta kama garuruwan Telskurf da Musqelet na wani dan lokaci ya kasance a zaman mai tsada domin sun kashe mayakan ISIS 80, suka lalata motocinsu 25.