Barrister Ali Gulak wanda a da shi ne yake ba tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara akan harkokin siyasa ya kwatanta gwamnatin APC da tafiyar hawainiya.
Ali Gulak yace akwai bukatar shugaba Buhari ya sauya salon tafiyar gwamnatinsa tunda yanzu shugaba ne na kowa.
Yace da APC ce jam'iyyar adawa amma yanzu tana gwamnati yayinda PDP ce ta zama jam'iyyar adawa. Ali Gulak yace saidai har yanzu APC bata san itace a karagar mulki ba. Tana cigaba da farfaganda kamar tana adawa ko kuma tana neman zabe.
'Yan Najeriya suna cikin kunci. Babu abinci. Tattalin arziki ya rugurguje. Da kyar ake biyan albashin ma'aikata. A jihar Adamawa an yi wata hudu ba'a biya albashi ba.
Ali Gulak ya yadda an soma samun zaman lafiya amma kuma akwai wata babbar rashin lafiya wato yunwa wadda bata san babba da yaro ba. A kasuwa kowa barci yake yi domin babu mai saya balle a sayarwa.
Saidai 'yan APC a martanin da suka mayar suka ce ba abun mamaki ba ne idan 'yan PDP na kuka yanzu. Alhaji Ahmed Lawal sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC a jihar Adamawa yace ko yaron dake goye ya san an samu sauyi yanzu. A fannin tsaro an samu cigaba. Abun da shi ma shugaba Buhari ya tabbatar.
Ga karin bayani