Fitacciyar ‘yar wasan kwallon kafar duniya ta mata Brandi Chastain, mai shekaru 47, 'yar kasar Amurka. Wadda tayi suna a lokacin wasan zakaru na cin kofin duniya na ‘yan-mata a shekarar 1999, ta bada kwakwalwar ta don gudanar da bincike. Masana dai na ganin cewar mafi akasarin mata da ke buga kwallon kafa kan samu wasu cututtuka da suka hada da ciwon mantu, da rawar jiki bayan wasu shekaru idan girma ya zo musu.
A cewar Brandi, idan na mutu bani da sauran bukatar kwakwalwa ta, don haka babu illa idan na bada ta don a gudanar da bincike da samo magani ga wannan matsalar da haryanzu ba’a iya gano sanadiyar ta ba. Ta kara da cewar, ta fara wasan kwallon kafa tun tana karama, kuma a lokacin da take buga ma makarantar ta wasa ta samu hadari na buguwar kai har sau biyu. Amma bata tunanin cewar wannan nada wata alaka da matsalar da take fuskanta na yawan mantuwa. Tana ganin akwai bukatar a iya gano meke haddasa wannan cutar ga mata, don mafi akasarin maza masu buga wasan kwallon kafa basu samun wannan matsalar, don haka akwai bukatar a iya gano wace irin matsala ce da kuma ganon banbancin illar wasan kwalo a tsakanin maza da mata.
Tace fatar ta dai shine masu bincike a tsangayar binciken hallitar dan’adam ta jami’ar Boston, suyi amfani da kwakwalwarta yadda ya kamata, don gano matsalar da ke haifar da wannan cuta musamman ga mata. A cewar masu gudanar da binciken, baza’a iya gano sanadiyar cutar ba idan anyi amfani da kwakwalwar mace mai rai, sai wadda ta mutu. Ita dai Brandi, ta sa hannu da cewar idan ta mutu, ta yadda dangin ta su bada kwakwalwar ta ga masu binciken. Hakan dai yasa wasu suma sun bada tasu kwakwalwar bayan sun mutu.