Al’ummar kasar New Zealand, sun fara kada kuri’a don neman ra’ayin ‘yan kasar wajen sake tsarin tutar kasar. Suna dai ganin cewar akwai bukatar canza yadda tutar take daga yadda take a yanzu, inda take dauke da hoto mai nuna hadin gamayyar kasashen turai, suna ganin kamata yayi ace tana nuna al’adun kasar.
An dai bude kofar kada kuri’ar wanda ake sa ran za’a kwashe makonni 3 kamin a tattara ra’ayoyin ‘yan kasar. Wanda ake sa ran idan Allah, ya kaimu ranar 24, ga wannan watan na Mayu itace ranar karshe. Ana dai sa ran idan aka hada sakamakon, kuma aka samu ra’ayin ‘yan kasar masu so a canza tsarin tutar kasar su kafi rinjaye, to bashakka kasar zata zama kasa ta farko a fadin duniya da ta taba canza tutar ta bisa tsarin demokaradiyya, tsarin zabi na al’umah.
Masu fashin bakin siyasa, sun bayyanar da cewar kimanin sama da mutane milliyan 4.7, ne zasu kada kuri’un su, inda ake ganin kamar mafi akasarin mutane zasu zabi barin tutar yadda take. Ana dai sa ran za'a kashe kimanin kudi da suka kai dallar Amurka milliyan $27M inda wasu ke ganin hakan a matsayin barna.