Masu iya magana kance “Baki shi ke yanka wuya” a wannan zamani na yanar gizo da kafofin sadarwa na zamani, sukan iya kai mutun ga wani hali da bazai yi tsammani ba. Yanzu haka dai wata karamar yarinya mai shekaru 12, na fuskantar tuhumar manyan laifufuka. Sau da dama mutane kanyi amfani da wadannan a matsayin hanyar bayyanar da halin da suke ciki kodai na jin dadi ko rashi.
Ita dai wannan yarinyar, tayi amfani da wasu zannunuka da kan bayyanar da halin da mutun ke ciki, wanda ba sai mutun ya furta magana ba. Ita dai yarinyar yar makarantar sakandire ta rubuta sako a shafin zumunta na “Instagram” na makarantar su, Fairfox a jihar Virginia ta nan kasar Amurka, inda sakon yake cewa “Ka sameni a laburari ranar Talata 🔫 🔪 💣” sai hoton bindiga, wuka da bom.
Amfani da tayi da bindiga, wuka da bom, na nuna cewar zata yi wani mummunan abu kenan a makarantar ta su, jami’an tsaro sun shiga cikin maganar don gano dalilin da yasa yarinyar ta aika wannan sakon. A cewar mahaifiyar yarinya, ‘yar-ta ta aika wannan sakon ne ba don tanada niyar yin wani mugun abu ba, ta aika wannan sakon ne a dalilin zalintar ta da akayi a makarantar, cikin bacin rai ta aika wannan sakon. Yanzu dai haka kotu zata duba wannan kamin a yanke mata hukunci dai-dai da abun da ta aikata.