Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Louis van Gaal Da 'Yan Wasan Manchester United Sun Ba Da Kunya


Masana tamaula sun bayyana wasan da Manchester United ta yi jiya alhamis da abokiyar tsamarta Liverpool, a gasar cin kofin Europa League, a zaman wasa mafi muhimmanci gare ta a wannan shekarar. A saboda haka ne ma aka yi tsammanin cewa manajanta da ‘yan wasanta duk zasu hadu su nuna kwazonsu sosai ta yadda magoya bayan United zasu koma gidajensu da farin ciki.

A maimakon haka, sai wasan ya kasance wani karin misali na yadda Manchester United ta kasa tabuka komai a wannan shekarar. Liverpool ta doke ta da ci 2-0.

Louis Van Gaal da ‘yan wasansa sun fito gaban magoya bayan Liverpool su dubu 40 da ‘yan canji a kai, cikin ruwan sanyi suka mika wa ‘yan Liverpool abinda suke kwadayi tun lokacin da aka hada kungiyoyin biyu a kan zasu kara a gasar cin kofin na Europa League.

A wannan kakar kwallo da United take farantawa magoya bayanta a wasu lokuta, amma a wasu take matukar harzuka su, wannan gasa ta Europa League watakila it ace hanya mafi sauki da zata iya kaiwa ga shiga gasar cin kofin zakarun kulob kulob na Turai, domin zai yi mata wuya ta samu shiga gasar ta hanyar Firimiya Lig a bana.

Wannan gasa ta Europa League ba ta yasarwa ba ce kamar yadda aka sani a baya, musamman ga ita kungiyar Manchester United wadda ta kasa samun sukunin cewa uffan game da wadanda zasu kasance a saman firimiya lig a bana.

Amma abin mamaki daga farko har karshen wasan na jiya alhamis, ‘yan Liverpool ne suka taka rawar kayyade yadda wasan zai kasance. Ba don irin bajimtar da mai tsaron gida na Manchester United, David de Gea, ya nun aba a jiya, da watakila wasan nan za a tashi ne da ci 5 da babu.

Abinda ya daure ma masana kwallon kafa kai shine an kasa gane wane irin shiri ne van Gaal yayi na tinkarar wasan jiya domin ba a gani a filin wasa ba. Mutumin da a can baya ya saba lallasa ‘yan wasan Liverpool, sai ga shi ya mika musu nasara cikin sauki, kuma ba don bajimtar mai tsaron gidan nasa ba, da kusan za a ce ko tsammani ba za a yi ma kungiyar a karawa ta biyu da zasu yi ba.

A yanzu, Manchester United ba ta da wani dan wasan dake haskawa in ban da De Gea. Irin natsuwa da kokarin da ya nuna wajen taren ruwan kwallaye daga Coutinho, Jordan Henderson, Daniel Sturridge da Nathaniel Clyne, ba kadan ba ne. Ba domin wannan bajimta ba, ko labara United ba zata kai ba.

Akwai ayar tambayoyi da yawa a kan Louis van Gaal bayan irin wannan wasa na jiya, kuma zai yi wuya a ce zai sake komowa a shekara ta uku a zaman manajan Manchester United. A yanzu dai kam, tamkar kungiyar Manchester United ba ta da wata alkibla ce, kuma dole duk laifi ya komo kan van Gaal.

Liverpool ba ta haye ba tukuna. Akwai karawa ta biyu da ‘/yan Manchester United a Old Trafford. Amma zai yi matukar wuya ma United ta juya akalar wannan bugu na jiya alhamis, sai fa idan manajanta da ‘yan wasanta zasu canja salo, su canja hali.

Bai kamata a ce kungiya kamar Manchester United tana wasa irin wannan ba.

XS
SM
MD
LG