Baman baman da suka tashi a sananniyar kasuwar Maiduguri, da ake cewa Monday Market sun kashe fiye da mutane hamsin.
Wakilin Muryar Amurka a Maiduguri ya ce bama-baman sun tashi ne da misalin karfe hudu na la'asar.
Mutanen da dama sun jikatta, to amma hukumomi ba su bayyana yawan wadanda su ka jikattan ba.
Wannan kasuwa ta na daya daga cikin wuraren da 'yan harin kunar bakin wake su ka kaiwa hari a ranar Asabar.
Fiye da mutane dari da arba'in ne su ka ji rauni a hare-haren.
Babu kungiyar da ta yi ikirarin cewa ita ke da alhakin kai harin, to amma ana tsammanin 'yan kungiyar Boko Haram ne ke da alhakin kai harin, domin galibi su kan auna kasuwa da wasu wuraren da jama'a ke taruwa.
Sau biyu kungiyar Boko Haram ta yi kokarin mamaye Maiduguri a bana, to amma sojoji da 'yan yakin sa kai na farar hula, da ake cewa civilian JTF su ka fatattake su.
A halin da ake ciki kuma shedun gani da ido sun ce jiya Talata mayakan Boko Haram su ka kai hari kan garin Ngamdu. Kamfanin dillancin labarai da ake kira Reuters, ya ba da labarin cewa an kashe mutane da dama.