Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Bom Ya Tashi a Maiduguri


Bom. (File Photo)
Bom. (File Photo)

An sake samun tashin wani bom a birnin Maiduguri, bom din ya tashi ne a kasuwar Monday, kuma ana zargin cewa an ajiye wannan bom din ne a wata jaka.

Kasuwar Monday, dai idan ba'a manta ba a asabar din da ta gabata ta fuskacin irin wannan harin bom, a yau din nan mutane da dama sun rasa rayukansu sanadiyar tashin bom din wasu da dama kuma sun samu raunuka.

Kasuwar ta Monday na cikin hatsaniya sanadiyar tashin bom din kuma an rufe kasuwar.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin, amma yana kama da na kungiyar Boko Haram dake tafka ta'asa da ta'addanci a arewacin Najeriya.

A halin yanzu, sojojin kwance da suka kunshi na Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru na cigaba da kwace yankuna da garuruwa daga hannun mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG