Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kan Wani Kauye A Jihar Borno


Sojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar Borno
Sojojin Najeriya masu yin sintiri a Maiduguri, Jihar Borno

Wasu mutanen da ake zaton ‘yan kishin Islama ne sunkai farmaki kauyen Chibok a Jihar Borno, suka kashe mutane akalla 10 mabiya addinin kirista.

Wasu mutanen da ake kyautata zaton ‘yan kishin Islama ne sun fantsama a wani kauyen dake arewacin Najeriya suka kashe mutane akalla 10 mabiya addinin kirista.

Mazauna kauyen Chibok a Jihar Borno sun ce ‘yan bindiga sun kutsa cikin kauyen ran asabar da daddare suka kai farmaki kan kiristocin. Shaidu sun ce wadannan mahara sun yanka mutanen suka kuma kona gidajensu.

Har yanzu jami’an gwamnatin Najeriya ba su tabbatar da bayanin wannan harin ba, amma wani jami’i yace watakila aikin kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun dora ma kungiyar Boko Haram alhakin mutuwar mutane fiye da dubu 3 tun shekarar 2009 a lokacin da ta yi yunkurin kafa tafarkin Islama a arewacin Najeriya. Wuraren da ta ke kai wa hari sun hada da ofisoshin ‘yan sanda da majami’u.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG