WASHINGTON, DC —
Hukumomin Najeriya da kuma wasu shaidun gani da ido sun ce wani dan kunar-bakin-wake ya kara motar da aka zuba nakiya ciki da wata majami’a a garin Kaduna na arewacin kasar, ya kashe mutane 7, ya kuma haddasa hare-haren ramuwar gayyar da suka yi sanadiyyar mutuwar wasu mutanen su biyu.
Dan harin ya abka kan majami’ar St. Rita dake unguwar Malali a Kaduna cikin wata motar jif a lokacin da aka taru ana ibada yau lahadi da safe. Masu aikin gaggawa sun garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibitoci. Shaidu sun ce a bayan harin, Kiristoci matasa da suka fusata sun fito kan tituna dauke da adduna da sanduna inda suka lakkada duka ma wasu Musulmi biyu ‘yan acaba har lahira.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai hari kan wannan majami’a.
A can baya, kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai harin bam da na bindiga a kan majami’u da dama cikin shekara guda da ta shige. A watan Yuni, kungiyar ta dauki alhakin hare-haren bam uku kan majami’u a jihar Kaduna, wadda ke tsakiyar kasar a dab da inda Najeriya ta rabu biyu tsakanin arewaci inda Musulmi ke da rinjaye da kuma kudanci inda Kiristoci ke da rinjaye.
Hukumomin Najeriya su na dora ma kungiyar Boko Haram alhakin kisan mutane fiye da dubu daya da dari biyar, ciki har da ‘yan sanda da jami’an gwamnati kama daga shekarar 2009. Da alamun ‘yan kungiyar su na enma ne su kafa irin ta su fassarar tsarin shari’ar Musulunci a arewacin Najeriya.